Daga Maryam Adamu Mustapha
Kungiyar Sanatocin Arewacin Nigeria ta tabbatar wa al’ummar Arewa kudurin su na magance matsalolin su dangane da wasu shawarwari da manufofin da gwamnatin tarayya ta fitar da su .
Kadaura24 ta ruwaito cewa Sanatocin sun bayyana hakan ne a matsayin martani ga matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na mayar da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya, FAAN da wani bangare na babban bankin Najeriya CBN daga Abuja zuwa Legas.
‘Yan Arewan sun nuna damuwarsu kan yadda aka karkatar da wasu kudaden da aka ware a kasafin kudin 2024, inda suka yi kira ga wakilansu a Majalisar kasa da su tashi tsaye wajen dakile duk wani yunkuri na kawo cikas ga yankin Arewa.
Sai dai a wata sanarwa da kakakin ta ya fitar, Sanata Suleiman Kawu Sumaila, mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu, kungiyar ta ce ta himmatu wajen ganin ta magance matsalolin da ‘yan Arewa ka iya fuskanta sakamakon matakin da gwamnatin tarayya ta dauka.
Kungiyar ta ce a matsayinta na mai wakiltar jama’ar yankin a matakin kasa, ya zama wajibi ta yi duk mai yiwuwa wajen magance matsalolin da ake fama da su na karkata da wasu kudade a cikin kasafin kudin 2024, da mayar da wasu hukumomin tarayya daga Abuja zuwa Legas.
“A matsayinmu na wakilan jama’a a matakin kasa (Majalisar Dattawa), mun himmatu wajen ganin mun magance matsaloli da kare ra’ayoyin ‘yan mazabarmu dangane da wasu shawarwari da tsare-tsare da gwamnatin tarayya ta fito da su a kasafin kudin 2024, da mayar da wasu hukumomin tarayya daga Abuja zuwa Legas.”
A cewar kawu Sumaila, a cikin sanarwar, kungiyar ta fahimci mahimmancin kyautata dangantaka tsakanin gwamnati da ’yan kasarta.
Ya bayyana cewa, kungiyar ta su na kokarin daukar matakan da suka dace don yin sulhu domin magance matsalolin da suka taso, ta hanyar yin amfani da dokokin kasa da kuma kundin tsarin mulkin Nigeria.
“ mun tabbatar wa ‘yan Arewa cewa mun dauki damuwarsu da muhimmanci kuma muna tattaunawa da abokan aikinmu domin magance wadannan al’amura yadda ya kamata. Mun yi imani da karfin tattaunawa da hadin gwiwa wajen kawo sauyi mai kyau ga al’ummarmu.
“A tsawon wa’adin mulkinmu, babban burinmu shi ne bayar da shawarwari don kyautata jin dadin jama’ar da muke wakilta, mun fahimci muhimmancin rawar da muke takawa a matsayin wani tsani tsakanin al’umma da gwamnatinsu, “in ji sanarwar a sassa.
“Mun gamsu da cewa al’ummar da muke wakilta suna da matukar hakuri da da mu. Yanzu lokacin mu ne na neman ci gaba da ba su goyon baya da fahimtar juna a wannan mawuyacin lokaci, za mu yi aiki don magance matsalolin da ke gaban al’ummar mu don su amfana da tsarin dimokuradiyyar mu,” in ji sanarwar.
Daga nan sai kungiyar ta bukaci ‘yan Arewa da su kasance masu hakuri yayin da suke lalubo hanyoyin tattaunawa, da yin shawarwari cikin lumana, da samar da matakan shari’a don shawo kan wadancan matsaloli .