Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukuncin Shari’ar Zaɓen Gwamnonin jihohin Kaduna Gombe Kebbi da Nasarawa

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Kotun koli ta yi fatali da karar da dan takarar jam’iyyar PDP a gwamnan Kaduna, Isah Ashiru wadda ke kalubalantar nasarar gwamna Uba Sani.

Kotun ta kuma tabbatar da hukuncin da kananan kotuna suka yanke da ya tabbatar da nasarar Uba a zaben watan Maris din 2023.

A ranar 24 ga watan Nuwamba ne kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar da nasarar gwamna Uba Sani na jihar Kaduna.

Batun Masarautun Kano, Kwankwaso ya Fadi Matsayarsa da ta Gwamnati

Sai dai kotun sauraron kararrakin zabe a nata bangaren ta samu rarrabuwar kai game da cancantar karar.

Kazalika a zaman nata na yau, Kotun koli ta kori karar da dan takarar jam’iyyar PDP Aminu Bande ya daukaka domin kalubalantar nasarar gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi.

Kwamitin alkalan ya ce karar ba ta cancanta ba.

Gwamnatin Kano ta Magantu Kan Dokar Hana yi Lefe a Aure da Ake Ce-Ce Ku-Ce Akan ta

Haka zalika kotun kolin ta kuma ayyana Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Nassarawa.

Kotun dai ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP David Umbugadu ya shigar inda yake kalubalantar nasarar Abdullahi Sule.

Kwamitin alkalai ya yanke hukuncin bai daya inda ya kori ƙarar saboda rashin cancanta.

A ranar 2 ga watan Oktoba ne, kotun kararrakin zabe a Lafia ta soke nasarar gwamna Sule tare da ayyana David Ombugadu a matsayin wanda ya yi nasara.

Daga baya kuma gwamna Sule da jam’iyyarsa APC suka garzaya kotu domin kalubalantar hukuncin kotun kararrakin zaben.

Kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke ranar 23 ga watan Nuwamba ta soke hukuncin farko inda kuma ta ce Sule ne halastaccen gwamnan Nassarawa.

Kotun daukaka karar ta ce kotun kararrakin zabe ta yi kuskure wajen dogara kan hujjojin shaidun PDP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yan sanda a Kano sun lashi takobin samar da ingantaccen tsaro a ranar Takutaha

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori,...

Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Hutun Mauludi

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gobe Juma’a, 12 ga...

INEC ta yi Allah-wadai da masu yakin neman zabe tun kafin lokaci ya yi

Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta yi Allah wadai...