Gwamnatin Kano ta Magantu Kan Dokar Hana yi Lefe a Aure da Ake Ce-Ce Ku-Ce Akan ta

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta yi bayani ƙarara kan tanade-tanaden dokar aure da take ta janyo muhawara a jihar da sauran shafukan sada zumunta.

Gwamnatin Kano ta bakin kwamishinan shari’a na jihar Barista Haruna Isa Dederi ta ce tabbas akwai dokar da ta yi bayani dalla-dalla kan yadda ya kamata mutane su riƙa gudanar da auratayyarsu a jihar.

“Doka ce da aka ƙirƙire ta tun 1988, kuma a sashe na biyar na dokar wannan bayani yake.

A tattaunawarsa da BBC Haruna Dederi ya ce dokar ta yi bayani kan mene ne ya halasta da kuma mene ne aka haramta idan an tashi aure a jihar Kano.

Da dumi-dumi: Tinubu ya gana da Ganduje da shugabannin APC na Kano

“Ba iya lefe kawai dokar ta haramta ba, amma a yanzu shi ne abin da ya fi ɗaukar hankalin al’umma,” in ji kwamishinan.

“Lokaci zuwa lokaci akan sake bibiyar doka, domin sake mata fasali idan muƙatar hakan ta taso.

“Tsayin zamani da kuma buƙatuwar mutane kan sa a sauya doka, ko kuma a yi mata kwaskwarima. Kamar dai yadda ake yi wa kundin tsarin mulki na ƙasa,” in ji Barr. Dederi.

Ya ce a iya saninsa babu wanda ya gabatar da bibiyar wannan doka domin sabunta ta, ko kuma sauya mata fasali.

A cewarsa matuƙar akwai doka, duk tsayin zamani idan ba a yi mata gyara ba tana nan a matsayin doka babu mai sauya hukuncinta.

An tambayi Dederi kan me yasa dokar ta ɗauki kusan shekara 36 amma da dama cikin al’umma ba su santa ba?

Abba Gida-gida ya Fadi Rawar da Kwankwaso ya Taka a Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano

Ya ce ƙalubale ne masu yawa da suke janyo haka, inda ya fara da zayyana yawan dokokin da ake da su a tarayya da jihohi. ya kuma ba da shawarar kamata ya yi a haɗa kundin wuri guda domin taƙaita yawan dokokin.

Ƙalubale na biyu shi ne ɓangaren shari’a na buƙatar a riƙa wayar da kai kan irin waɗannan dokoki. Saboda ƙuduri baya zama doka sai ya bi matakai da dama, tun a lokacin matakan ya kamata a riƙa sanar da al’uma a kanta.

Kazalika idan majalisar dokoki ta jiha ta tabbatar da doka ya kamata a riƙa samar da sashe da zai riƙa shaidawa mutane dokar.

Masu aiwatar da dokar ma ya kamata su riƙa ilimantar da mutane game da dokokin da ake yi musu hukunci a kai, ba zai ranar da hukunci ya zo ba mutum ya ji ta a matsayin sabuwar doka a kansa.

Kwamishinna Haruna Isa Dederi ya amsa cewa akwai ƙarancin wayar da kan al’umma game da dokokin rayuwa da suka shafe su, wanda kuma haka aikin gwamnati ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...