Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce babu shakka za a sake duba batun masarautun Kano guda biyar da gwamnatin data gabata ta samar.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya raba masarautar Kano gida biyar tare da tsige Sarkin Kano na lokacin Alhaji Muhammadu Sanusi.
Gwamnatin Kano ta Magantu Kan Dokar Hana yi Lefe a Aure da Ake Ce-Ce Ku-Ce Akan ta
Bayan nasarar da jam’iyyar NNPP ta samu a zaben shekarar da ta gabata, Kwankwaso ya ce gwamnatin Engr Abba Kabir Yusuf za ta yi nazari a kan tsaga masarautun da aka yi.
Da yake yin wata hira a wasu gidajen Radio dake kano, bayan nasarar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu a kotun koli, jagoran jam’iyyar ta NNPP ya sake bayyana cewa babu shakka za a sake duba batun masarautun Kano.
Da dumi-dumi: Tinubu ya gana da Ganduje da shugabannin APC na Kano
“Gaskiya yana daya daga cikin abubuwan da babu wanda ya zauna da ni don tattaunawa ya zuwa yanzu, amma na tabbata za mu zauna mu ga yadda za mu yi. Shin za a yarda, rushewa, gyara za a yi ko yaya? Za dai a sake dubawa, kuma ayi abin da ya kamata .
“Akwai abubuwa da yawa da aka yi su ba don cigaba jihar kano ba. An kawo su ne da wasu munanan manufofin da kowa da kowa a nan da masu sauraronmu suka sani.
“Wani lokaci kana zuwa da abubuwa masu kyau sai su zama marasa kyau, wani lokacin kuma ka kawo abubuwan da ba su da kyau sai su zama masu kyau. Don haka abin da na sani shi ne har yanzu ba a tuntube ni ba amma tabbas za mu zo mu tattauna mu ga abin da ya kamata a yi.”