Daga Rukayya Abdullahi Maida
A Ranar Alhamis din data gabata ne shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi ganawar sirri da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje da kuma shugabanni da kusushin jam’iyyar APC na jihar kano.
Wata majiya mai tushe daga jam’iyyar APC ta shaida wa Majiyar KADAURA24 ta NIGERIAN TRACKER cewa, a lokacin da jiga-jigan APC na Kano suka gana da shugaba Tinubu, ya yaba musu bisa kokarin da suke yi na bayar da gudumawarsu ga nasarar APC.
Dangane da batun jam’iyyar da makomarta a Kano, majiyar ta ce shugaba Tinubu ya bukaci shugabannin jam’iyyar da su je su sake farfado da jam’iyyar a Kano ta yadda za ta dawo da martabar ta don samun nasara a zabuka masu zuwa.
Batun Masarautun Kano, Kwankwaso ya Fadi Matsayarsa da ta Gwamnati
Dangane da batun hukuncin kotun koli da ya tabbatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf kuwa, majiyar ta shaida wa majiyar mu cewa shugaban ya shaida wa shugabannin jam’iyyar APC na kano cewa bai taba tsoma baki a hukuncin kotun koli da aka yi ba.
Dangane da makomar siyasar tikitin takarar Gwamna a jam’iyyar APC, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, dan takarar gwamna, da mataimakinsa Murtala Sule Garo, shugaban kasar ya shaida musu cewa zai ga abin da zai iya yi wajen saka musu, amma bai bayyana ainihin lokacin da zai yi hakan ba.
Shugaban Kasar ya kara da cewa bai yi yarjejeniya da kowa ko wata kungiyar siyasa ba, dangane da tabbatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano da kotun daukaka koli ta yi.
Gwamnatin Kano ta Magantu Kan Dokar Hana yi Lefe a Aure da Ake Ce-Ce Ku-Ce Akan ta
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito, a ranar 18 ga Maris, 2023, dan takarar gwamnan NNPP Alhaji Abba Kabir Yusuf ya samu nasara akan abokin takararsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna na APC. Inda Abba Kabir Yusuf ya samu kuri’u miliyan daya da dubu goma sha tara inda Gawuna ya samu kuri’u dubu 890 .
Sai dai APC ta garzaya kotun duk da dan takararta na Gwamna Gawuna ya taya Abba Kabir Yusuf na NNPP murna. A ranar 20 ga Satumba, 2023, kotun sauraren kararrakin zabe a Kano ta soke zaben Gwamna Abba bisa dalilan rashin sahihancin kuri’u 165, sannan ta bukaci INEC da ta ba wa Gawuna takardar shaidar cin zabe.
Da bai gamsu da hukuncin ba, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya garzaya kotun daukaka kara, wadda ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben ta yanke a baya a ranar 17 ga watan Nuwamba. Bayan rashin gamsuwa da hukuncin kotun daukaka kara, Gwamna Yusuf ya garzaya kotun koli, kuma a ranar 12 ga watan Junairu, 2024, kotun ta yi watsi da hukuncin da kananan kotuna suka yanke tare da tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben gwamnan jihar Kano.