Yadda Falakin Shinkafi ya Gudanar da Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa a Gidan Marayu

Date:

Daga Aisha Ibrahim

 

Yayin da mawadata ke gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarsu a wuraren shakatawa tare da ‘ya’yansu, Amb. Yunusa Yusuf Hamza Falakin Shinkafi ya banbanya Kansa da su, ta hanyar gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarsa a gidan Marayu na Nasarawa dake jihar kano.

Da yake zantawa da wakilin kadaura24 a wajen taron Falakin Shinkafi yace ya zabi ya gudanar da bikin ne da marayu domin sanya farin ciki a zukatansu da kuma tallafa musu.

Falakin Shinkafi

” Na zabi yin wannan biki ne a nan tare da wadannan marayun saboda mu jawo hankalin sauran al’umma su daina zuwa suna kashe kudade masu yawa da ‘yansu kadai, su rika tunawa cewa akwai wadannan bayin Allah da suke bukatar suma a sanya farin ciki a zukatansu”.

Da dumi-dumi: Tinubu ya gana da Ganduje da shugabannin APC na Kano

” Duk musulmi ya Sani Annabi Sallahu alaihi wasallam ya bayyana muhimmacin taimakon Marayu da kuma irin arzikin da ya jawo wa al’umma, don haka domin ne mu rike wadannan yara da muhimmacin gasket”.

Falakin Shinkafi Wanda kuma shi ne Jarman Matasan Arewacin Nigeria ya bukataci gwamnatoci da mawadata a cikin al’umma da su rika tallafawa marayun don saukaka musu halin da suke cikin . ” In ka taimaki ya’yan wasu kai kuma Allah ne zai taimaki naka lokacin da ka rasu.

Abba Gida-gida ya Fadi Rawar da Kwankwaso ya Taka a Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano

A jawabin ta Darakta Janar Bincike da adana muhimman bayanai ta gidan gwamnatin jihar Kano Nana Asma’u Jibril ta yawaba Falakin Shinkafin bisa yadda ya zabi gudanar da bikin Murnar zagayowar ranar haihuwarasa tare wadancan Marayun.

DG research Hajiya Nana Asma’u Jibril

Ta kuma bukatar sauran al’umma da su himmatu wajen taimakawa al’umma musamman Marayu saboda alfanun da hakan ke da shi a rayuwar al’umma duniya da lahira.

Ita ma a nata Jawabin Shugaba sake kula da gidan Marayun na Nasarawa Hajiya Aishatu Sani Kurawa bayan ta yabawa Falakin Shinkafi kan abubunwan alkhairin da ya Kai marayun ta yi kira ga sauran al’umma da su yi koyi da abun da yayi don samun tsira a duniya da lahira.

Ta kuma yabawa gwamnatin jihar kano bisa yadda take kula da marayun, Sannan ta ce akwai bukatar lokacin zuwa lokaci mutane su rika ziyarar gidan don ganin halin da marayun suke ciki don tallafa musu.

Bayan rabawa kananan yaran Cake an kuma raba musu Kayan wasa da sauran kula da tsaftar yara a wani bangare na bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Falakin Shinkafi Amb. Dr. Yunusa Yusuf Hamza.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...