Wani sabon nau’in sauro da ake yi wa lakabi da “steve,” wanda ya samo asali daga Kudancin Asiya, yana haifar da karuwar masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro a kasashen Afirka.
Kasashen African da sabon sauron yayi karuwa guda bakwai ne, da suka hada da Djibouti, da Habasha, da Kenya, da Najeriya, da kuma Ghana, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Abba Gida-gida ya Fadi Rawar da Kwankwaso ya Taka a Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano
Ba kamar sauran sauro na yau da kullun ba, “steve” yana bunƙasa ne a cikin birane kuma ba ya bukatar danshi mai yawa kafin ya hayayyafa.
Ganduje Ya Caccaki ‘Yan Siyasa Kan Lamarin Zaɓe a Najeriya
Wannan nau’in sauron na cizo da rana, yana da juriya ga magungunan kashe ƙwari na yau da kullun, kuma yana haifar da ƙalubale ga dabarun yaƙi da zazzabin cizon sauro a halin yanzu, in ji Dr Dorothy Achu shugabar WHO kan cututtuka masu addabar mutanen da ke zaune a yankunan duniya masu zafi na Afirka, inda ta ƙara jaddada wahalar ganowa da kuma kawar da wannan sauro mai saurin jure yanayin.
BBC Hausa