Ganduje Ya Caccaki ‘Yan Siyasa Kan Lamarin Zaɓe a Najeriya

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace ‘yan siyasa sune babbar matsalar Nigeria, musamman game da yadda ake gudanar da zabukan kasar.

Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da ya karbi bakuncin daraktar zabe da sa ido na jam’iyyar na hukumar zabe ta kasa (INEC), Hawa Habibu.

Ya ce duk da cewa rashin tsaro babban abin damuwa ne wajen gudanar da zabe, amma ‘yan siyasa sun fi zama hadari.

Abba Gida-gida ya Fadi Rawar da Kwankwaso ya Taka a Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano

“Na san daya daga cikin manyan matsalolin INEC wajen gudanar da zabe shi ne rashin tsaro. Mutane kuma na cewa INEC ce, amma ‘yan siyasa  suma matsala ce.

Kyautar Motar da aka Baiwa Jarumar Labarina Yasa Marubutan Kannywood Kokawa

“Don fahimtar ka’idoji da dokokin zabe akwai bukatar dan siyasa ya zama mai wayewa, cibiyoyinmu za su rika wayar da kan jama’armu lokaci zuwa lokaci ta yadda za su bi ka’idojin, kuma zai zama ta hanyar zamani .

“Mun kuma ba da umarnin cewa a dukkan ofisoshin jam’iyyarmu, tun daga mazabu zuwa kananan hukumomi, shiyyoyi da jihohi, dole ne a samu jami’ai.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...