Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa ba zai taba cin amanar mai gidansa, tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba.
Da ya ke jawabi ga magoya baya a Abuja, jim kaɗan bayan yanke hukuncin Kotun Ƙoli da ta tabbatar masa da zaɓen sa, Gwamna Yusuf ya nuna godiya ga Kwankwaso bisa kwazonsa na ganin cewa ba a zalunci al’ummar Kano ba.
A cewar Gwamna Yusuf; ” mu na godiya ga Allah da wannan gagarumar nasara da ya bamu. Mu na kuma godiya ga jagoran mu, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa kwazonsa na ganin cewa ƙuri’un da aka awa su ka kada ba a kwace musu ba.
Kyautar Motar da aka Baiwa Jarumar Labarina Yasa Marubutan Kannywood Kokawa
“Hakika Kwankwaso jagora ne kuma mu na alfahari da shi. Za mu ci gaba da yin biyayya kuma ba za mu taɓa cin amanar sa ba,” in ji Gwamnan.
Jirgi ya yi saukar gaggawa bayan fasinja ya gartsa wa ma’aikaciya cizo
Ya kuma godewa shugaban ƙasa Bila Tinubu da mataimakin sa, Kashim Shettima bisa nuna dattaku na kin saka baki a shari’ar, inda ya ce hakan ya kara wa kasar da kuma dimokuraɗiyya kima a idon duniya.
Gwamnan ya kuma godewa alkalan Kotun Ƙoli bisa abinda ya kira da “adalci wajen ganin sun baiwa mai gaskiya gaskiyar sa. Hakan zai kara gyara harkar zabe da dimokuraɗiyya a kasar,”
“Mu na matukar godiya ga al’ummar Kano bisa wannan soyayya da ake nuna mana. In sha Allah za mu bijiro da aiyukan alheri da za su kara habbakar arziki da ci gaba a jihar mu. Mun gode muku sosai,” in ji Gwamnan.