Kyautar Motar da aka Baiwa Jarumar “Labarina” Yasa Marubutan Kannywood Kokawa

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman

 

Kyautar Motar da aka baiwa jaruma Fatima Husaini wato Maryam ta cikin shirin “Labarana” yasa wani shahararrin marubuci a masana’antar kannywood mai suna Maje El-Hajeej Hotoro ya koka da yadda ake mantawa da Marubutan da suke rubuta Fina-Finan Hausa.

” Sau tari ana mantawa da Marubutan da sune suke bata lokaci wajen rubuta labarin Fina-Finan da ake ganin jaruman da suke taka rawa har su burge al’umma a lokuta daban-daban.

Maje El-Hajeej Hotoro ya bayyana hakan ne a sahihin shafinsa na Facebook.

Sarkin Kano Ya Magantu Kan Nasarar Gwamna Abba Kabir a Kotun Ƙoli

Ga abun da ya rubuta.

A RIKA TUNAWA DA MARUBUTA….

A wannan kafa ( Facebook) na ga ana yada cewa, wani bawan Allah mai kallon shirin Labarina ya gwangwaje Fatima Hussain (Maryam Labarina) da kyautar Mota Wadda kudinta ya kai Naira Miliyan Shida (6m).

Mutumin ya ce “Nayi mata kyautar motar ne sakamakon yadda ta nuna gudun dukiya a cikin shirin Labarina, hakan ya burgeni sosai”.

“A matsayina na marubuci ina kira da a rika tunawa da marubuta labarin finafinai waɗanda sune matakin farko na kowane fim”. Inji Maje El-Hajeej Hotoro

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kotun Hukunta ’Yan Kwaya Da Masu Kwacen Waya

“Malam Yakubu M. Kumo sannu da kokari, Malam Aminu Saira hannun ka yayi albarka”.

Sau tari ana baiwa jarumai kyaututuka saboda rawar da suka taka a Fina-Finan Hausa, ba tare da la’akari da cewa suna taka rawar da marubuci ya basu bace a cikin shirin fim din.

Fatima Husaini wato Maryam Labarina ta sami kyautar wata dankareriyar mota saboda yadda a fim din ta nuna dukiya bata dame ta ba. Kuma ta bi wanda bashi da komai a fim din.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...