Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da ke ta tabbatar da mutuwar mutuminnan da ya kwace wayar wata mata a zoo Road Mota ta buge shi yayin tsallaka titi a Kano.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar talatar nan.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce mutumin ya mutu ne a yau talata a asibiti kwararru na Murtala Muhammad dake birnin Kano.
Wani Mawaki a Kano ya Maka BBC Hausa a Kotu
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito, Bayan mota ta buge wani mutum da ya zare makami (dan buda) ya kwaci wayar wata mata, an gano cewa kashin bayansa ya karye kuma kansa ya fashe”, in ji kakakin ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa.
Sai dai daga bisani kakakin ‘yan sandan na Kano ya sake wallafa wani sako da ya nuna cewa mutumin da ya kwaci wayar yana cikin mummunan yanayi.
“Bayan Mun Kai shi asibiti likitoci sun tabbatar da cewa kashin bayan wanda ya kwaci wayar ya karye sakamakon bugewar da Mota ta yi masa”.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sha kama masu kwacen waya tana gurfanar da su a gaban kuliya.