Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf murnar nasarar da ya samu a kotun koli.
Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce hukuncin kotun koli nuni ne na zabin mutane da kuma dimokuradiyya da kuma shugabanni na kwarai da masu biyayya ga abin da masu zabe za su yi.
Wani Mawaki a Kano ya Maka BBC Hausa a Kotu
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran masarautar kano, Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Yanzu-yanzu: Barawon da ya kwaci waya Mota ta buge shi a Kano ya mutu – Yan sanda
A cewar sanarwar dake kunshe ta taya murna, Sarkin ya yabawa al’ummar jihar Kano bisa zabin da ya dace wanda zai tabbatar da ci gaba da tsare-tsare na cigaban jihar.
Daga karshe ya yi addu’ar Ubangiji Allah ya kare shi daga makiya na zahiri da badini, ya kuma ba shi kwarin guiwar cika alkawura da kuma gudanar da ayyukansa cikin himma da nasara.