Daga Aisha Aliyu Umar
Jam’iyyar APC a Kano sun ce sun rungumi ƙaddara game da hukuncin kotunƙolin Najeriya da ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.
”Allah ya sa hakan ne ya fi alkari, kuma muna bai wa ‘yan jam’iyar mu na APC tda sauran al’ummar jihar kano hakuri, tare da kiran a zauna lafiya”, in ji shi.
Sakataren jam’iyyar na jiha Ibrahim Zakari Sarina, ya shaida wa BBC cewa sun karɓi ƙaddara, suna kuma fatan hakan ya zame musu alkairi.
Yanzu-yanzu: Kotun Ƙoli ta tabbatar da Abba Kabir a matsayin Gwamnan Kano
Ya ce kuma suna kyautata wa Allah zato cewa tabbas hakan zai zama alkairi a gare su.
”A yanzu muna cikin alhini, kuma bai kamata mu ɗauki mataki a lokacin alhini ba, amma idan ƙura ta lafa, za mu zo mu zauna, mu shirya domin tunkarar zaɓen 2027”.
Tun da farko dai jam’iyyar ce ta yi nasara a kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara, kafin yau kotun ƙoli ta yi watsi da hukunce-hukuncen kotunan farkon.