- Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Jami’an tsaro da suka hadar da hadakar dukkanin jami’an daga hukumomin tsaro Nigeria sun tsaurara matakai a birnin kano, yayin da ake jiransa hukuncin Kotun Ƙoli kan shari’ar zaɓen gwamnan jihar kano.
Wakilin kadaura24 ta bamu labarin cewa an jibge tarin jami’an tsaro a kofar shiga gidan gwamnatin jihar kano domin tabbatar da tsaro a gidan.
Da dumi-dumi: Kotun Ƙoli ta Yanke Hukuncin Shari’ar Zaɓen Gwamnan Lagos
A wasu daga cikin titunan birnin ma an jibge tain jami’an tsaro domin shirin ko ta kwana bayan kammala yanke hukuncin Kotun Ƙoli Ƙoli zata yi nan da wani lokaci kankani.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito kwamishinan yan sandan jihar kano CP Husaini Gumel ya sha alwashin daukar matakan ba sani ba sabo a kan duk wanda ya karya doka bayan kotun kolin ta yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan jihar.
Tarihin Alƙalin Da Zai Jagoranci Yanke Hukuncin Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano
Jama’a da dama sun zauna a gidajen su don gudun abun da ka je ya zo bayan hukuncin, duk kuwa da yadda hadar jami’an tsaro ke sintiri a titunan birnin kano domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.