Daga Rahama Umar Kwaru
Kotun Ƙolin Nigeria ta tabbatar da gwamnan jihar Lagos Babajide Sanya- Olo a matsayin halastacce gwamnan jihar.
Kotun Ƙolin ta mai alƙalai guda 7 ta yanke hukuncin ne a yau juma’a.
Tarihin Alƙalin Da Zai Jagoranci Yanke Hukuncin Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano
Kadaura24 ta tabbatar Kotun Ƙolin ta jaddada hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe da kotun daukaka kara suka yanke, Inda sukai watsi da karar da LP ta shigar suka kuma tabbatar da gwamna Sanwo Olu a matsayin halastacce gwamnan jihar Lagos.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa jam’iyyar LP da dan takarar ta Rhodes Vivour ne suka daukaka karar bayan da suka ga cewa basu gamsu da hukuncin Kotun daukaka kara ba.