Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Kotun koli ta tabbatar da zaben Bala Mohammed a matsayin gwamnan jihar Bauchi.
Mai shari’a Ibrahim Saulawa wanda ya karanta hukuncin ya yi watsi da karar da Sadique Abubakar na jam’iyyar APC ya shigar bisa rashin cancanta.
Da dumi-dumi: Kotun Ƙoli ta Yanke Hukuncin Shari’ar Zaɓen Gwamnan Lagos
Gwamna Bala Muhammad dai shi ne wanda yayi nasara a kotun sauraren kararrakin zaben gwamna jihar Bauchi kuma ya sake yin nasara a kotun daukaka kara,yau kuma Kotun Ƙoli ta tabbatar masa da nasarar sa.