Shirin KSADP Zai Gina Cibiyoyin Tattara Madarar Shanu 60 a Kano

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Shirin bunkasa noma da makiyaya ta jihar Kano, KSADP, wanda bankin ci gaban Musulunci da asusun rayuwa da asusun LLF, suke Daukar nauyi ya bayar da kwangilar da ta kai NairaN3, 962, 457, 126. 12, domin gina cibiyoyin tattara madarar shanu guda 60 a fadin jihar Kano.

Kwangilolin, an ba da su ga wasu kamfanoni hudu na yan asalin jihar kano, tare da bukatar su kammala aikin cikin tsawon watanni 12 a kowane aiki.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran shirin KSADP, Ameen K Yassar ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.

Talla

Sanarwar ta ce kowace cibiyar tattara Madarar za ta kasance tana da rijiyar burtsatse da aka sanya mata kawun famfo, kuma ta zama mai amfani da hasken rana, sannan ta zama mai dauke da tanki mai cin ruwa lita 20,000; kantin kayan abinci (abinci, magunguna) da dai sauransu.

INEC ta Sanya Ranar da Zata Gudanar da Zabukan Cike Gurbi a Kano

Bugu da kari, a kowacce matattara madara za a sanya tankin ajiye madarar mai cin lita 250 dauke da na’urar sanyayawa mai amfani da hasken rana da kuma Kayan gwaje-gwaje don inganta tattara madarar.

Jim kadan bayan bayar da kwangilolin wanda ya gudana bisa sanya idanun ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, kodinetan kula da ayyukan noma da kiwo na jihar Kano Malam Ibrahim Garba Muhammad ya bayyana cewa “kawo irin wannan aikin a Najeriya zai taimaka wajen dinke barakar da ke tsakanin makiyaya da manoma ”.

Yan sanda sun karya ta labarin sace mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja

“Daya daga cikin manyan matsalolin da masana’antar kiwo ke fuskanta shi ne rashin wadatacciya da kuma ingantacciyar madara. Wannan aikin na samar da wajen tattara madarar shanu, anyi shi ne da nufin tabbatar da samar da madara mai inganci da lafiya, ta hanyar sanya na’urar sanyi. Wannan zai ba da tabbacin sayar da ita da kuma samun kudin shiga ga makiyaya,” in ji shi.

Malam Ibrahim ya bukaci kamfanonin da aka baiwa kwangilar da su gudanar da ayyuka masu nagarta, su kuma gama aikin akan lokacin da aka amince musu, domin tabbatar da kwarin gwiwar da suke da shi akan su.

Idan za a iya tunawa, a watan Satumba, 2022, Hukumar Noma da Makiyaya ta Jihar Kano ta bayar da kwangilar gina cibiyoyin tattara madarar guda 40 a Kano, a matsayin wani mataki na cin gajiyar dimbin kiwo da jihar ke da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Daga Zakaria Adam Jigirya     Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...