Daga Aisha Aliyu Umar
Kotun koli ta tsayar da ranar Juma’a 12 ga watan Junairu, 2024 domin yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan jihar Kano tsakanin jam’iyyar NNPP da APC.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kotun kolin ta aikewa dukkanin lauyoyin bangarorin biyu a yau laraba.
Malam Shekarau Ya Yiwa Abba da Gawuna Nasiha Kan Hukunci Kotun Ƙoli
Sanarwar tace, Kotun ta bada umarnin cewa kowane bangare kada ya tura Lauyoyi sama da biyu.
Tun a ranar litinin din data gabata jaridar kadaura24 ta bada labarin cewa kotun ta tsara zata yanke hukuncin na kano a ranar juma’a 12 ga watan janairun shekara ta 2024.