Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya yi kira da mabiya da shugabannin NNPP da na APC su rungumi hukuncin da kotun kolin ƙasar za ta yanke a matsayin ƙaddara.
Shekarau ya ce, ya yi imani da cewa babu wani zagi ko cin zarafi ko kuma kalaman ɓatanci da za su sauya hukuncin da kotu za ta yanke, ko kuma su sa a bai wa wani nasara a yayin hukuncin.
![](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2023/11/IMG-20231113-WA0014-1-212x300.jpg)
Shekarau ya yi wannan kira ne a wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels a wani shirin siyasa.
Da dumi-dumi: Kotun Koli ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa
Tun a watan Maris ɗin 2023 ne ake ta sa-toka-sa-katsi a kotu tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma Nasiru Yusuf Gawuna kan kujerar gwamnan jihar Kano.
Shekarau ya ce “duk mutumin da ke bin siyasa ta, yasan siyasar zaman lafiya da kwanciyar hankali nake yi. Ina ɗaukar abokan siyasata abokaina ba tare da duba banbancin siyasa ba.