Daga Aisha Aliyu Umar
Ministar ma’aikatar jin kai Dr. Betta Edu da aka dakatar a ranar Talata ta isa hedikwatar Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa (EFCC) bisa zargin almundahanar Naira miliyan 585 a ma’aikatar ta.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a ranar Litinin ne shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Edu.

An zargi ministan da biyan kudaden jin kai a wani asusu na wata mata ta sirri.
Da dumi-dumi: Kotun koli ka iya yanke hukuncin shari’ar zaɓen Kano da Legas ranar Juma’a
An ce Naira miliyan 585 an yi amfani da shi ne don biyan tallafi ga marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Legas, Cross River da Ogun.
Edu dai ita ce minista ta farko da aka dakatar daga mukaminta, tun bayan rantsar da mambobin majalisar zartarwa ta shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a watan Agusta na bara.