Daga Rukayya Abdullahi Maida
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ke Kano ta ce ta kammala dukkanin wasu shirye-shiryen domin gudanar da zaɓen cike gurbi na Kunchi/Tsanyawa, Kura/Garin Malam da Rimin Gado/Tofa na majalisar dokokin jihar da aka shirya gudanarwa a ranar 3 ga watan Fabrairu.
Majiyar kadaura24 ta Prime times ta rawaito, Amb.Abdu Zango, Kwamishinan Zabe (REC) a jihar, ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a hedikwatar hukumar da ke Kano a ranar Talata.
“Mun shirya tsaf domin gudanar da zaben tare da kwararrun jami’an mu, don gudanar da sahihin zaben cike gurbi a kananan hukumomi shida na jihar.

“Za mu gudanar da zabe a rumfunan zabe 66 a fadin kananan hukumomin shida.
“Duk mutumin da ba shi da katin zabe na dindindin ba zai yi zaben wallahi ba,” in ji shi.
Gwamnatin Kano tana baiwa kananan hukumomin damar tasarrafi da kudadensu – Abdullahi Sanusi Getso
Ya ce tuni hukumar ta tura wasu muhimman kayayyaki da ba su da muhimmanci sosai ga daukacin kananan hukumomin da abin ya shafa.
Zango ya bayyana cewa za a yi amfani da na’urar BVAS a yayin sake gudanar da zaben da nufin tabbatar da sahihin zabe da gaskiya.
“Mun shirya tare da baiwa jami’anmu ilmin zabuka na yau da kullun domin gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci a ranar 3 ga watan Fabrairu,” in ji shi.
Kwamishinan na INEC ya yaba da kokarin ‘yan sanda na samar da tsaro da ake bukata kafin zaben cike gurbi da kuma lokacin zaben.