Da dumi-dumi: EFCC ta Gayyaci Ministar Jin kai Bette Edu

Date:

Hukumar yaki da masu karya tattalin arziki (EFCC) ta gayyaci Ministar Jinkai, Beta Edu, wadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar kan badakar kudi Naira miliyan 585.

Gayyatar ta zo kasa da mintuna 30 da Bola Tinubu ya sanar da dakatar da Edu ta hannun kakakinsa, Ajuri Ngelale.

Wani jami’in EFCC ya tabbatar wa da wakilinmu cewa, “Tuni aka aike mata da takardar gayyata a hukumance, kuma muna sa ran za ta zo domin kara haske kan. Don haka muna sa ran zuwa nan ba da dadewa ba,” in ji wani jami’in na EFCC.

Yanzu-yanzu: Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai, Betty Edu

Binciken da muke yi kan zargin ba zai yi tasiri ba idan ba a dakatar da ministar ba, domin dakatarwar za ta ba mu ’yancin yin aikinmu sosai, yadda shugaban kasa ya umarce mu,” in ji shi.

Yanzu-yanzu: Kotun Ƙoli ta Yanke Hukunci kan Shari’ar zaɓen gwamnan jihar Benue

Tinubu ya dakatar da Ministar Jinkai, Beta Edu kan badakalar N585m
Zargin N37bn: Sadiya ta kai kanta EFCC
Jami’in ya shaida wa Aminiya cewa tun da farko hukumar ta bayar da shawarar dakatar da Beta Edu domin ba da damar gudanar da bincike kan badakalar kudin.

Majiyar ta ci gaba da cewa, hukumar ta fara aikin bincike ne nan take bayan shugaban kasar ya sa a gudanar da cikakken bincike kan zargin biyan tallafin Naira miliyan 585.189 da aka ware wa marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Kuros Riba, Ogun da Legas zuwa wani asusu na sirri.

Ba mu samu jin ta bakin kakakin EFCC, Dele Oyewale game da lamarin ba, saboda bai amsa kiran da wayar wakilinmu ba.

Kungiyoyin farar hula, lauyoyin masu fafutuka, jam’iyyun adawa da sauransu sun yi ta kira da a sallam Beta kan badakalar.

Aminiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...