Daga Rukayya Abdullahi Maida
Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON ta kara wa’adin lokacin biyan kuɗin aikin hajjin shekara ta 2024.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, mai dauke da sa hannun mataimakiyar daraktar hukumar ta NAHCON, Fatima Sanda Usara.
Sanarwar ta ce sabon wa’adin na yanzu shi ne 31 ga Janairu, 2024, maimakon 31 ga Disamba, 2023.

Sanarwar ta ce, an kara wa’adin ne saboda yadda malaman addini, Hukumomin jin dadin jiha, Gwamnonin Jihohi, da sauran masu ruwa da tsaki suka bukata.
Wakokin Kannywood 5 Da Suka Fi Shahara A 2023
“Saboda haka, NAHCON tana da yakinin cewa kafin cikar sabon wa’adin, tare da hadin gwiwar hukumomin Jin dadin alhazai mutane zasu sami damar biyan kudin aikin Hajjin 2024,” inji ta.
Ta bayyana cewa amincewar da gwamnatin tarayya ta yi na tsawaita wa’adin zai ba da dama ga mutane su sami damar sauke faralin a bana.