Ina alfahari da Salon shugabancin ka , Tinubu ya fadawa Ganduje

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa yana matukar alfahari da salon jagorancin da Dr. Abdullahi Umar Ganduje yake nunawa a matsayinsa na shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin da Dr Abdullahi Umar Ganduje da mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) suka kai masa ziyara a Legas ranar Alhamis.

Idan za’a iya tunawa Shugaba Tinubu yana gudanar da hutun kirsimeti da sabuwa a Legas.

Talla

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban Jam’iyyar APC na kasa kan harkokin hotunan masu motsi da taruka, Aminu Dahiru, wanda kuma ya aikowa kadaura24.

Tinubu ya ce, “Ina alfahari da shugabancinku da sabbin tsare-tsare da kuka bullo da su musamman Cibiyar ci gaba.

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Sauyawa Ma’aikatar Mata ta Jihar Suna

“Ni ma dole in gode muku da yadda kuka kawo zaman lafiya a jihar Ondo a cikin jam’iyyar.” Inji shugaba Tinubu

Da yake jawabi, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa shugaba Tinubu kan goyon bayan da yake baiwa shugabannin jam’iyyar.

Ganduje ya ce, “Mai girma shugaban kasa, dole ne in yaba maka bisa goyon baya da hadin kai ga shugabancin jam’iyyar.

“Alkawarin da kuka yi na ba Najeriya alkibla da kuma dakile tasirin cire tallafin ya yi yawa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...