Zamu tsaya Kai da fata wajen tallafawa iyalan yan kungiyarmu da suka rasu – Shugaban FAIS yan ajin 1999

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

 

Kungiyar tsofaffin daliban tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci (FAIS) ta Jamiar Bayero, da suka Kammala karatu a shekarar 1999, ta jaddada kudirinta na tallafawa iyalan wadanda suka rasu dake cikin kungiyar domin inganta rayuwarsu yadda ya kamata.

 

“Kungiyar na aiwatar da irin wannan taron ne, domin tunawa da wadanda suka Rasu da tallafawa iyalansu da kuma,wadanda basu da karfi a cikin Kungiyar tare kuma da sada zumunci”.

Shugaban Kasa Tinubi ya Taya Shugaban APC Na Kasa Ganduje Murnar Cika Shekaru 74 da Haihuwa

Shugaban Kungiyar Alhaji Nura Ibrahim ne ya bayyana haka a lokacin gudanar da taron kungiyar na shekara-shekara wanda ya gudana a halkwatar hukumar kula da Harkokin yawan bude ido ta jihar kano.

Talla

Yace, Kungiyar za ta ci gaba da gudanar da irin wannan taron don sanin halin da ‘Ya’yenta suke ciki da kuma, taimaka musu domin su ma su ji dadin gudanar da rayuwarsu kamar kowa.

Sakataren Kungiyar Aliyu Umar Aliyu, ya bayyana cewa, gudanar da irin wannan taron, zai kara hada kan alumma da bunkasa Zumunci tsakanin Juna ta hanyar tattaunawa da juna.

Wani sashi na mahalarta taron

Aliyu Umar yace,Kungiyar Dalibai ‘Yan Ajin Shekarar (1999) Kansu a hade yake da juna a kodayaushe,inda yace,amma duk da haka za su ci gaba da gudanar da taron har tsawon Rayuwarsu.

Wani sashi na mahalarta taron

A jawabinsa Shugaban Gidan Rediyon tarayya pyramid, Malam Abba Bashir Wanda daya ne daga cikin jigajigan wannan Kungiya,ya Shawarci Kungiyar da ta Samar da tsarin da za,a rika ciyar kudin da mutum yake da halin bayarwa a matsayin tallafi ta Asusunsa na Banki koda karshen wata ne,maimakon shawarwarin da wasu daga cikin yankungiyar suka bayar na cewar,Kungiyar ta Samar da wani kasuwanci da za’a rika juya kudin Kungiyar domin tallafawa ‘Ya’yanta da iyalan wadanda suka rasu.

Talla

Abba Bashir yace, idon aka ce,za’a fara irin wannan tsarin juya kudi to zai iya haifar da nakasu da koma baya a cikin Kungiyar.

‘Ya’yan Kungiyar da dama ne suka halarci taron tare da ba da Shawarwari daban.daban domin ciyar da Kungiyar ta tsafaffin Daliban,Daga cikin wadanda suka halarci taron,akwai Alh. Aliyu Diso da Dangaladiman Buhindu Bagudu Murtala Abubakar da Wazirin Danbbata Mustapha Shehu da kuma Mata da dama Wanda ‘Yankungiyar ne da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...