Tsofaffin dalibai nada rawar da zasu taka wajen gyaran makarantun firamari – Alh. Kyauta Adamu

Date:

Daga Rakayya Abdullahi Maida

 

Kungiyar tsofaffin daliban makarantar firamare ta kwalli tace tsaffin dalibai nada rawar da zasu taka a gyaran makarantun firamari don inganta harkokin ilimi da kuma gyaran makarantu.

 

“Muna Kira ga shugaban hukumar ilimin Bai daya na jihar Kano (Subeb) da ya alamtawa Gwamnatin jihar kano cewa ya kamata ta samar da wani gurbi ga tsaffin Daliban makarantu masu kwazo Wurin tallafawa makarantun da su kayi karatu domin inganta su”.

Talla

Shugaban hada Kan dalibai na Kungiyar tsaffin dalibai na makarantar kwalli sifeshiyal firamari Kyauta Adamu Shi ne yayi wannan Kira yayin jawabinsa a taron shekara-shekara da Kungiyar ta Saba gabatarwa.

 

Alh. Kyauta yace taron yan aji na 1975 ne suka shirya shi kafin Hado Kan sauran Yan babin Ajujuwa wadanda sukayi makarantar kwalli firamari don ganin abinda za suyi a sabuwar Shekara ta 2024.

Ganduje@74: Tarihin Dimokaradiyyar Nigeria ba zai Cika ba sai an sanya Shugaban APC na kasa – Dr. Yusuf Jibril JY

Kyauta yace makasudin yin hakan Shi ne sada zumunci da kuma tallafawa ilimi ta kowace fuska, kamar yadda Yan Ajin 75 suka samar da Naaura Mai kwakwalwa, dakin karatu (library) da Littattafai, da sauran Abubuwa masu Mahimmanci da zasu taimakawa harkar koyo da koyarwa a makarantar kwalli firamari.

A Jawabin Shugaban Aji na 1975 Hon. Justice Faruq Lawan Adamu yace shekaru goma sha shida kenan tunda aka kafa Kungiyar suna bakin kokari Wajen ganin makarantar kwalli firamari ta inganta.

 

Inda ko a wannan Karon ya gabatar da magunguna da suka samarwa makarantar don bada agajin gaggawa ga dalibai marasa lafiya ko kuma malamansu.

 

Kazalika Bai gushe ba sai da yaja hankalin wadanda basa zuwa taron a kowace Shekara cewa, Kar mutum ya damu da me zai bayar abinda kawai suka fi maida Hankali da bawa muhimmanci Shi ne dabbaka zumunci.

Talla

Malama Hasana Umar Aminu ita ce Shugabar makarantar kwalli sifeshiyal firamari a wannan lokacin ta yabawa tsaffin daliban na Ajin 1975, da irin cigaban da suka kawo a makarantar.

Batun makarantar kwalli Kam koda gwamnatice tayi aikin da akayi yanzu a iya cewa tayi aikin kusan shekaru goma, kasancewar za’a iya Tara makarantu da dama ba’a samu wadda takai Inganci da samun gyara ta dalilin tsaffin dalibai ba, Wanda nan gaba sai dai a Kira makarantar kwalli da ICT Ba sifeshiyal ba sakamakon fasaha da kwarewar daliban da kanzo sahun farko ba iya Kano ba harma da kasa baki daya, don haka wannan abin a yaba ne inji Shugabar makarantar kwalli sifeshiyal firamari Malama Hasana Umar Aminu.

A karshe Shugabar tsaffin daliban na Ajin 1975, kana kuma Mai magana da yawun Kungiyar tsaffin daliban na makarantar kwalli sefeshiyal firamari Haj. Gambo Ahmad Mustapha, ta godewa kafatanin wadanda suka samu halartar taron tsaffin daliban Maza da Mata,in da tayi Fatan Allah yasa taron yafi haka anan gaba, ya kuma maida kowa gidanshi cikin koshin lafiya.

Taron dai yasamu halartar manyan Mutane Maza da Mata daga maaikata daban-daban, inda Kungiyar ta karrama mutane biyu daga cikin Shugabani ta kuma yi alkawarin daukar mutum biyu a kowace Shekara don karramasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...