Injiniyoyi nada gudunmawar ba da wa wajen cigaban Kano da Nigeria – Sarkin Bichi

Date:

Daga Abubakar Lawan Bichi

 

Mai Martaba Sarkin Bichi Alh Dr Nasir Ado Bayero yace injiniyoyi nada Mahimmiyar rawar takawa wajan cigaban Nigeria dama duniya bakin daya saboda sana’arce mai mutukar Mahimmanci ga al’ummar.

Sarkin da ya bayana haka ne a yayi da ya karbi bakuncin shugaban Kungiyar Injiniyoyi na duniya Injiniya Mustapha Balarabe a fadarsa.

Alh Dr Nasir Ado Bayero yace zaman Injiniya Mustapha Balarabe Shugaban Kungiyar Injiniyoyi na duniya abun alfahari ga duk wani dan jihar Kano da bakaken fata bakin daya.

Talla

Sarki ya horin sabon Shugaban Kungiyar Injiniyoyi na duniya Injiniya Mustapha Balarabe daya kawo abubawan da zasu ciyar da jihar Kano da Nigeria baki daya gaba domin mukamin daya samun mikamine Wanda zai rika yi mu’amula da al’ummar duniya kala kala.

Hukuncin Kotun Koli: ‘Yan sanda sun yi sabon gargadi ga al’ummar jihar Kano

A Jawabinsa Shugaban Kungiyar Injiniyoyi na duniya Injiniya Mustapha Balarabe yace ya je fadar Sarkin domin sanar da shi mukami daya samun na Shugabanci Kungiyar Injiniyoyi na duniya da kuma yiwa sarki Ta’aziyar rasuwar yar uwar Hajiya Hauwa Ado Bayero.

Injiniyoyi Mustapha ya godewar Sarkin bisa bawa daya daga cikin Yan Kungiyar Injiniyoyi na Kasa Sarauta Injiniya Murtala Mukkadas tare da tarbatarwa Sarkin zama jakada na garin.

Tun da farko Shugaban Kungiyar Injiniyoyi na Jahar Kano Injiniya Ibrahim Usman Dederi yace sun je fadarsa Sarkin da Bichi domin Kyautata alaka Kungiyar da Masarautar Bichi da kuma gabatar daya daga cikin yan jihar Kano Injiniya Mustapha Balarabe Wanda ya zaman Shugaban Kungiyar Injiniyoyi na duniya domin neman goyon bayan dasa Albarka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...