Daga Aisha Aliyu Umar
Gwamnatin jihar kano ta bayyana cewa bata san daga inda aka samo umarnin Kotu na rufe asusun gwamnatin jihar ta Kano ba.
Kadaura24 ta rawaito wata sanarwa da ma’aikatar shari’a ta jihar kano ta fitar, tace ta lura da wata takarada dake yawo a shafukan sada zumunta wadanda ke nuna cewa wata Kotu dake Abuja ta umarci da a kulle asusun na gwamnatin jihar sakamakon kin biyan diyyar masu shaguna a filin idi.
Sai dai ma’aikatar ta shari’a tace har Yanzu bata samu wannan Hukunci a hukunance ba, wanda shi ne zai gasgata Ingancin hukuncin dake yawo a shafukan sada zumunta.

Ma’aikatar tace ta umarci lauyoyin su da su gudanar da bincike akan wanann batu dake yawo a shafukan sada zumunta.
Hukuncin Kotun Koli: ‘Yan sanda sun yi sabon gargadi ga al’ummar jihar Kano
Ranar Laraba ne dai wata Kotun tarayya dake Abuja ta umarci wasu bankuna guda 24 da su rufe asusun gwamnatin jihar kano dake bakunansu sakamakon kin biyan diyyar Naira Biliyan 30 ga masu shaguna a filin masallacin idi na Kofar mata dake Kano.