Daga Rahama Umar Kwaru
Gamayyar yan majalisun tarayya na jam’iyyar NNPP sun ce babu wata tattaunawa da jam’iyyarsu take yi da wata jam’iyyar domin hadawa a Nigeria.
“An jawo hankalinmu a kan wani labari da wasu kafafen yaɗa labarai ke watsawa cewa jam’iyyarmu ta NNPP ta fara tattaunawa da PDP da ma wasu jam’iyyun don yiwuwar haɗewa da su”.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Hon. Abdulmumini Jibril Kofa ya sanyawa hannu a madadin sauran yan majalisun, wadda aka aikowa kadaura24.
Hukuncin Kotun Koli: ‘Yan sanda sun yi sabon gargadi ga al’ummar jihar Kano
“Sam babu ƙamshin gaskiya a wannan labarin, ƙarya ce tsagwaronta. Matsayin NNPP ba ɓoyayye ba ne a kan batun yin alaƙa da wasu jam’iyyu, inda muka ce a shirye muke mu yi aiki tare, mu yi ƙawance ko ma haɗaka da APC, PDP, LP ko ma kowacce jam’iyya”. A cewar Kofa
“Amma a halin yanzu babu wata tattaunawa da muke yi da kowacce jam’iyya kuma ba mu halarci kowanne irin taro don tattauna yiwuwar yin haɗaka da PDP ko ma kowacce jam’iyya ba. Wannan aikin masu neman tayar da zaune tsaye ne kuma abin da suke ƙoƙarin yi ke nan”.