Daga Abdurrashid B Imam
Shugaban kungiyar shugabannin jami’an hulda da jama’a na jam’iyyar APC dake arewa maso gabas, wanda kuma shi ne kakakin jam’iyyar a Kano Hon. Ahmad S Aruwa ya yi kira tare da jan hankalin yan majalisar jihar kano da kada su kuskura su sahalewa gwamnan kano ta tafi hutun da ya ce za shi.
“Ina tabbatarwa al’ummar jihar kano cewar ko ina Abba ya shiga, indai jam’iyyar APC ta karɓi mulkin jihar kano babu makawa sai mun dawo da shi don ya girbi abinda ya shuka”.
Aruwa ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24 a kano.

Hon. Aruwa ya yi alkawarin cewa zasu bayarwa duk dan kasuwar jihar Kano da akai musu rusau da zarar Nasiru Yusuf Gawuna ya tabbata matsayin gwamnan jihar kano nan ba da jimawa zasu maidawa da kowa wajan sa tare da rage musu wani abu daga cikin asarar da akai musu .
NJC ta amince da ƙarin girma ga alkalin da ya yanke hukuncin zaɓen gwamnan Kano a kotun daukaka kara
” Rusau din da wannan gwamnatin ta yi ya dawo da harkokin kasuwanci baya a jihar kano, sannan ya nuna cewa ita wannan gwamnatin ba Mai kishin yan kasuwa da sauran al’ummar jihar kano ba ne”. Inji Aruwa
Daga karshe ya tunasar da al’ummar jihar kano cewa yana da kyau su kara dagewa da yin addu’o’in samun nasara Dr. Nasiru Gawuna a Kotun Ƙoli domin cigaban jihar kano.