Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Mai Martaba Sarkin Gaya Dakta Aliyu Ibrahim ya karbi Bakuncin Shugaban Kungiyar Asibitoci na Dawakin Kudu Farfesa Jamilu Ismail Ahmad yayin zaman fadar na yau Laraba a fadarsa dake Garin Gaya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hadimin Sarkin Gaya kan harkokin yada labarai Com. Ubaliyi ya aikowa kadaura24.
Dakta Aliyu Ibrahim ya kuma yi kira ga Al’ummar Masarautar ta Gaya kan Muhimmancin Kula da lafiya tare da ziyartar Asibitoci da zarar Anji alamu na rashin lafiya.
” Lafiya ita ce komai don haka Muna kira ga al’ummar mu da su daina wasa da abun da ya shafi lafiyar su, su rika zuwa asibitoci don samun kulawar likitoci akan lokaci don inganta lafiyar su”. A cewar Sarkin Gaya
Ya Kara da cewa masu hannu da shuni su ci gaba da taimakawa wajen kula da inganta harkar lafiya.
Mai Martaba Sarkin Gaya ya nada Amb. Ibrahim Haruna BBY a matsayin Jarman Gaya
” Akwai bukatar masu hannu da shuni su rika sanya hannu jari a sha’anin kula da lafiyar al’umma , Saboda yin hakan zai taimakawa al’umma ya kuma ragewa gwamnati nauyin kula da lafiyar al’ummar”. Inji Dr. Aliyu Ibrahim
Farfesa Jamilu Isma’Il ya bayyana cewa sun zo Fadar ne domin Neman tabarrakin Sarki, tare da yiwa sarki Godiya da ban gajiya bisa wakilci da aka tura wajen taron bude sabon asibiti a Garin Dawakin kudu.
Haka Zalika, Shugaban Darikar Kadiriyya Nasiriyya na shiyar Gabas da Kano Alsheik. Adnan Sa’ad Al-maliki yazo da jama’arsa domin yiwa sarki Godiya da ban gajiya bisa wakilci daya tura wajen Taron Maulidi da aka yi makon daya gabata.