Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kimanin lauyoyi masu zaman kansu 500 ne suka yi alƙawarin kare dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna a kotun koli.
kadaura24 ta rawaito Joseph Onwudiwe, mai magana da yawun lauyoyin a karkashin kungiyar masu kula da dimokuradiyya da doka ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja a yau Talata.

Mista Onwudiwe ya ce an yi hakan ne domin inganta dimokuradiyyar kasar.
“Yan Najeriya sun lura sosai da halin da ake ciki a jihar Kano dangane da zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga Maris.
Harin Yan Maulidi: Ya’yana 6, duk an kashe su —Magidanci
“A matsayinmu na kungiyar da ke da alhakin kare mutuncinmu da dabi’unmu na dimokuradiyya, yanzu ba mu gamsu da hare-haren maganganu marasa dadi da ake kaiwa bangaren shari’a ba.
“Kuma wani yunƙuri na bata wa Kotun suna ba. Ba za mu sake naɗe hannayenmu a matsayin lauyoyi ba kuma mu kalli yadda ake ci gaba da cin zarafi da cin mutuncin sashen shari’a ba,” in ji shi.