Daga Aisha Aliyu Umar
Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya ce makarantu da dama a jihar Katsina sun zama sansanin ‘yan bindiga sakamakon rufe su da akai saboda matsalar tsaro.
Kadaura24 ta rawaito Gwamna Radda a bayyana haka ne a ranar Asabar din da ta gabata yayin bikin yaye dalibai karo na 7 a jami’ar Gwamnatin tarraya ta Dutsi-ma da ke jihar Katsina, inda ya bayyana cewa babu ilimi idan babu tsaro.
“Da yawa daga cikin makarantun da suke kananan hukumominmu an rufe su saboda ‘yan fashin daji, wasu lokutan kuma, makarantu su kan zama makoyar ‘yan fashi,” in ji shi

“Wannan ne ya sa muka kafa kungiyar samar da tsaro don lura da al’ummar Jihar Katsina domin yaki da rashin tsaro da kuma samar da wata gidauniya da zata taimakawa matasanmu don su sami Ilimi da cigaba.”
Tirkashi! Gwamnati Ta Sa Jirgin Shugaban Kasa A Kasuwa
Radda wanda shi ne babban mai masaukin baki a bikin, ya tunatar da daliban da aka yaye cewa su sani don sun kammala karatu bai kamata su tsaya da neman Ilimi ba, kamata yayi su Kara zage damtse wajen neman ilimi don samar da cigaba mai dorewa a cikin al’umma.
“Ina so in yi amfani da wannan dama wajen tabbatar wa mai girma shugaban kasa da al’ummar Jihar Katsina cewa mun himmatu wajen inganta Ilimi a jihar. A cikin watanni 6 gwamnatina ta dauki malamai sama da 7,000 aiki, ta kashe sama da Naira biliyan 2 wajen gyara makarantu 361, ta gina makarantun sakandire 75 a karkashin shirin AGILE, sannan ta himmatu wajen kaddamar da makarantun na model guda 3 kamar yadda nayi alkawari a yakin neman zabe na.

“Za mu mai da hankali kan sake fasalin ilimi baki daya tare da kafa sashin kula da ingancin ilimi don tabbatar da sa ido da tantance tsarin ilimin mu.