Daga Hauwa Abdullahi
Wasu matasa a unguwar Kurna dake karamar hukumar fagge sun gudanar da zanga-zangar lumana a safiyar wannan rana ta Larab, Saboda nuna fushin su kan zargin da suke yiwa jami’an yan sanda na kashe Wani mutum a unguwar ba tare da ya aikata laifi ba.
Da yake zantawa da jaridar kadaura24 guda cikin masu zanga-zangar mai suna Ibrahim Naziru kalla yace suna gudanar da zanga-zangar ne sakamakon yadda wasu jami’an tsaro wadanda suke kyautata zaton yan sanda sune sun harbi wasu mutane uku a unguwar su ba tare da sun aikata laifi ba.
” Acan kasan unguwar mu ne ake fada wanda tazarar wurin da unguwar mu kurna bayan makaranta ta kai akalla kilo mita daya, amma suka zo unguwar mu a cikin babur din adaidaita sahu , ganin yadda muka fito domin tsare unguwar mu saboda dama haka muke yi, damu mutane cikin farin kaya da makamai yasa matasanmu suka fara cewa basa so a tunanin su yan daba ne, hakan yasa su kuma suka fara farbi har suka harbe mana mutane uku”.
Yace cikin mutane uku da aka harba yanzu haka daya daga cikin su yanzu haka ya rasu sauran biyun kuma suna asibiti suna samun kulawar likitoci. Ya kara da cewa shi wanda aka kashe sunansa salisu kuma mutumin kirki ne da a koda yaushe yake ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya.
” Yanzu mun tare wannan hanyar ne har sai an cika mana kudirori uku da muke da su, na daya Rundunar yan sanda ta fito ta wanke wanda aka kashe, na biyu kuma a hukunta wanda ya kashe shi ba bisa ƙa’ida ba, sai na uku da muke neman a baiwa Iyalansa diyyar ransa tun da dai ba mai laifi ba ne”. A cewar sa
Matasan sun roki gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Babban sufeton yan sanda na kasa da su tabbatar an yi musu adalci kan wadancan kudirorin nasu guda uku.
Domin jin ta bakin Rundunar yan sandan jihar Kano mun nemi Jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda jihar kano SP Abdullahi Haruna kiyawa ta yawar tarho Amma har lokacin da muke hada wannan rahoto wayarsa a kashe ta ke , amma zamu cigaba da bibiya don jin ta bakin Rundunar.