Tinubu ya gaji bashin aikin tituna na Naira Tiriliyan 6 daga Gwamnatin Buhari – Ma’aikatar Ayyuka

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

Ma’aikatar ayyuka ta tarayya ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ta gaji bashin sama da naira tiriliyan 6 na ayyukan titunan kasar daga tsohuwar gwamnatin, Muhammadu Buhari .

 

Dave Umahi, Ministan ma’aikatar yace Tinubu ya amince da kashe Naira biliyan 300 don gudanar da ayyukan gyaran hanyoyi cikin gaggawa a fadin jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya.

Ma’aikatar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, inda ta ce daga cikin Naira biliyan 300, an ware naira biliyan 100 ne domin gudanar da ayyuka a jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja, yayin da Naira biliyan 200 aka ware domin ci gaba da gudanar da mafi yawan ayyukan titunan da aka gada a fadin kasar nan.

 

A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya ba da umarnin cewa dole ne a fara gudanar da ayyukan kafin ranar 1 ga Disamba, yayin da yace dole a lura da duk matakan da suka dace.

Rasuwar Darakta Aminu S Bono: Forodusa Abdul Amart na shan yabo

“Shugaban tarayyar Najeriya yana sane da yanayin da hanyoyin kasar nan suke cikin tun a ranar 29 ga watan Mayun 2023. Bisa la’akari da irin kokarin da gwamnatin da ta shude ta yi na samar da ababen more rayuwa . Zamu yi duk mai yiyuwa wajen gyara hanyoyin da suka lalace a fadin Nigeria”.a cewar sanarwar

“Shugaban kasa Tinubu baya korafin kalubalen da ya gada a kusan dukkanin bangarorin tattalin arziki, musamman yadda ya shafi hanyoyinmu, amma ya jajirce kamar yadda ya sha alwashin tunkarar matsalolin ba tare da la’akari da tarin bashin da aka gadar masa ba ba akalla sama da Naira Tiriliyan Shida, wanda galibi na aiyukan hanyoyi ne a Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...