Kasurgumin Dan daba a Kano Hantar Daba ya mika kansa ga yan Sanda

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Hantar Daba Kwanar Diso ya kai kansa Shelkwatar ‘yan Sandan Kano bayan neman sa da take Ruwa a Jallo.

Kadaura24 ta rawaito mai magana da yawun Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da hakan a sahihin shafinsa na Facebook.

Sanarwar tace Hanyar Daba ya Kai kansu Rundunar yan sandan ne bisa rakiyar mahaifiyarsa da yan uwansa a jiya litinin, Inda ya yi alkawarin daina harkokin daba, tare da shan alwashin bada gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar kano.

” Ina nadamar abubun da nayi a baya, don haka ina kira ga duk wanda na taba zalunta ta kowacce fuska da ya yafe min, sannan ina rokon rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanya ni cikin wadanda ta ke yiwa afuwa”. A cewar sa

Hanyar Daba ya kuma bada tabbacin cewa yana da yara sama da dari da shi ne shugaban su Kuma ya yi alkawarin kawo su suma su tuba , sannan kuma ba za’a sake samun fadan Daba a unguwar Hausawa Gwale zuwa Kofar Na’isa ba.

Tinubu ya gaji bashin aikin tituna na Naira Tiriliyan 6 daga Gwamnatin Buhari – Ma’aikatar Ayyuka

Sanarwar da kiyawa ya fitar ta nuna cewa yanzu haka hantar daba yana karkashin kulawar rundunar su, don haka duk wanda yasan yana da korafi akan shi to ya je helkwatar rundunar domin abi masa hakkinsa.

Kwamishinan yan Sanda na jihar kano CP Hussaini Gumel ya yabawa al’ummar jihar bisa yadda suke baiwa rundunar hadin kai ta hanyar kai mata sahihan bayanai, Inda ya rokesu da su cigaba da taimakawa rundunar don cigaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...