Daga Abubakar Lawan Bichi
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudininta na cigaba da Samar da ruwan sha mai tsarta ga Jama’a jahar.
Manajan daratan hukumar Samar da ruwan sha ta jihar Kano Injiniya Garba Ahmad Bichi ya bayyana haka yayi taron masu ruwan da tsaki wand ya kunshi masu unguwani da Yan Kwamitin ruwa na Karamar hukumar Bichi.

Yace gwamnati jihar Kano ta kashe miliyoyin kudi domin gyara madatsar ruwa ta watari don samar da ruwan ga al’ummar Kananan hukumomin Bagwa,Bichi, Dawaki Tofa, Tsanyawa, da kuma Karamar hukumar Ungogo.
Injiniya Garba Ahmad Bichi ya kara da cewa hukumar samar da ruwa ta jihar Kano ta Shirya taro tartaunawa ga masu ruwa tsaki domin ingarta Samar da ruwan sha ga Jama’a Jaharnan.
Shugaba Tinubu ya Magantu Kan Matsin Rayuwar da yan Nigeria Suke Ciki
Shugaban Kwamiti Samar da ruwan sha na Karamar hukumar Bichi Mallam Aminu Halilu Bichi yace Kwamiti nasu izuwa yanzu ya gyara fayaf fayaf na ruwa wanda suka fashe, ya kuma ce zasu cigaban da ayyuki tukuru domin gani ruwa ya wadata a dukkan fadi Karamar hukumar Bichi.
A Jawabinsa Darata Mai kula da tara kudi na Hukumar ya Samar da ruwa ta Jahar Kano Alh Umar Bala Ibrahim yace Gwamnati Jahar Kano na kashe miliyoyin kudaden domin samar da ruwan sha ga Jama’a, Don haka yayi Kira da Jama’a dasu rika biyan kudin ruwa domin kuwa da kudin ake biyan albashi da kuma gyare gyare a matatu ruwa.

Taro ya sami halarta dukkan masu ruwa da tsaki aka samar na ruwan sha na Karamar hukumar Bichi.