Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Wata kotun majistare a Minna da ke jihar Neja ta yanke wa wani mutum mai suna Gambo Adamu hukuncin ɗauri na shekara guda bisa zargin damfarar surukarsa.
Surukar tasa, wadda bazawara ce ta garzaya kotu ne tare da koken cewa surukin nata ya yi mata wala-wala bayan karɓar kuɗin da suka kai naira miliyan biyar daga hannunta da sunan zai haɗa aure tsakaninta da tsohon shugan ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Malam Gambo ya riƙa shaida wa surukarsa cewar yana shirya aure tsakaninta da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Ta shaida wa kotu cewa wata rana Gambo ya kai mata naira 100,000 a matsayin sadakinta, da huhun goro ɗaya da kuma soyayyiyar kaza da nufin cewa kyauta ce daga tsohon shugaban ƙasar, bayan ya yi mata ƙaryar ɗaura auren.
Yadda muka dakile yunƙurin Bazoum na guduwa daga Nijar – Sojojin Ƙasar
Ta ce a matsayinta na Amariya, ta yi ta dakon sabon angon nata ya zo ya ɗauketa amma ta ji shiru.
Yayin da ba ta ganshi ba ne ta yanke shawarar kai surukin nata gaban kotun domin ta shiga tsakaninsu.
Alƙalin kotun, mai shari’a Ibrahim Musa Zago, ya ɗaure surukin nata wata 12 a gidan yarin, da zaɓin tarar naira 100,000, saboda samunsa da laifin cuta, laifin da ya saɓa da sashe na 322 na kundin final cod.
Haka kuma kotun ta umarci Malam Gambo ya biya surukar tasa naira miliyan biyu a matsayin diyya.