Hukumar kula da Dakunan karatu ta kasa ta bada tallafin kayan karatu a Karamar Hukumar Garun Malam

Date:

Daga Safiyanu Dantala Jobawa

 

Hukumar kula dakunan karatu ta kasa reshen jihar Kano (National Labraries of Nigeria) ta mika tallafin kayan koyo-da-koyarwa na zamani don inganta harkar ilimi ga al’ummar garin Jobawa dake karamar hukumar Garun malam.

Babban jami’i a hukumar na jihar kano Alh Sunusi Abdullahi Nasarawa ne ya jagoranci mika kayan, Inda ya ce sun bada gudunmawa kayan karatun ne a ƙoƙarin su na kara bunkasa Ilimi a yankin.

Yadda aka bude sabon babin sauraren daukaka kara tsakanin Musa Iliyasu Kwankwaso da Yusu Datti 

“Duba da irin gudunmawar da dagacin Jobawa ke bayarwa musamman a fannin ilimi ya sa muka shigo da yankinsa don bada wannan tallafin, kuma muna fatan wadannan kayan karatu zasu taimaka wajen kara cusa dabi’ar son karatu ga daliban wannan yankin”.

A madadin sauran jami’an hukumar ta Dakunan karatu na Kasa reshen jihar Kano, Malama Fatima Tahir, sun bukaci da ayi amfani da kayan ta yadda ya kamata, tare da kira ga iyaye musamman ma mata da su kara jajircewa kamar yadda aka san su da shi wajen kula da karatun ya’yan su.

Talla

A karshe dagacin Jobawa, Umar Inuwa ya gode wa hukumar dakunan karatun a bisa zabar yankinsa da aka yi don shigar da su tsarin bada tallafin kayan koyo-da-koyarwa a wannan shekarar.

Talla

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...