Daga Rahama Umar Kwaru
Hukumar dakile yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce an gano mutane 15,060 da ake zargin sun kamu da cutar mashako (diphtheria) a kasar.
NCDC ta bayana hakan ne a daidai lokacin da ta ke karin haske kan matakin da kasar ke dauka kan bullar cutar diphtheria da ta sake kunno kai a kasar.

Darakta Janar na NCDC, Dokta Ifedayo Adetifa, ne ya bayyana haka a taron bada bayanin halin da ake ciki game da cutar ta mashako a ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce ya zuwa ranar alhamis an samu rahoton mutane 15,060 da ake zargin sun kamu da cutar diphtheria tare da 9,478 da aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin kananan hukumomi 137 da ke cikin jihohi 20 ciki har da babban birnin tarayya.
Kotu ta ɗaure mutumin da ya yi wa surukarsa ƙaryar aura mata Buhari
Jihar Kano ce ke kan gaba a yawan masu dauke da cutar da suka kai mutane 7,747, sai jihar Yobe da take biye mata da yawan mutane 841.
Ya ce bayanan sun kuma nuna cewa kashi 71.5 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar yan tsakanin shekaru 1 zuwa 14 ne, inda jarirai ba su kai kashi daya cikin dari na wadanda suka kamu da cutar ba.
Dangane da barkewar cutar, Adetifa ya ce NCDC ta tura jami’an bayar da agajin gaggawa zuwa jihohin da abin ya shafa, don san ido a garurun da kuma bayar da taimakon gaggawa.

Sai dai ya koka da yadda kalubalen tsaro ya ke hana jami’an zuwa wasu garuru dake kananan hukumomin da abin ya shafa.
Ya ce cibiyar kula da annobar ta Jihar Kano, ta yi wa yara 1,111,310 allurar rigakafin, da kuma yara 544,737 allurar rigakafin Pentavalent a kashi na biyu.
Ya kara da cewa haka ma Kaduna, Bauchi, Borno, Katsina, Jigawa, da Yobe sun yi wa dubban daruruwan yara allurar rigakafin ta hanyar gudanar da aikin rigakafin.