Ba zamu sassauta ba wajen hukunta duk basaraken da aka samu yana taimakawa ‘yan bindiga a Katsina – Dikko Radda

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

 

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, a ranar Juma’a, ya sha alwashin daukar matakin ba Sani ba sabo akan duk wani kwamishina, basaraken gargajiya ko kuma wani mai rike da mukami a gwamnatinsa da aka kama yana taimakawa ‘yan ta’adda a jihar.

Radda ya jaddada cewa duk da yake yaki yan ta’adda abun ne mai hatsarin gaske, Amma ya bada tabbacin ba zai zaman sulhu da duk wani dan fashin daji ko kungiyar su ba .

Talla

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga, kungiyar ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, rahotanni sun nuna cewa akwai kungiyoyi sama da 120 a yankin.

Gwamnan ya shaidawa manema labarai a wata tattaunawa da aka yi da su a Transcorp Hilton, cewa gwamnatin sa ta ci gaba da kokarin ganin an dakile aiyukan da suke yi a jihar.

Kotu ta ɗaure mutumin da ya yi wa surukarsa ƙaryar aura mata Buhari

Ya ce, “A yayin da nake magana da ku, akwai wasu sarakunan gargajiya da ake zargi, kuma yanzu mun sa a fara bincike akan su. Ba mu keɓe kowa ba. Ina gaya muku cewa hatta kwamishinoni na ko duk wanda yake cikin gwamnatin mu, indai an same shi yana da hannu a cikin wani laifi to ba za mu sassauta masa ba wajen hukunci .

“Muna maganar rayuwar mutanen Katsina ne, ba mutum daya ba. Babu wani mutum daya da ya fi mutane miliyan 10 muhimmanci, musamman ma rayukan wadanda ba su ji ba ba su gani ba dake kauyuka. Muna iyakacin kokarinmu mu akan yadda za mu iya tattara bayanai da dama, tare da bayanan sirri da muke samu daga hukumar DSS domin mu kama mu kuma gurfanar da wadanda aka samu da laifi .

Talla

“Tun da na zama gwamna, babu wata rana da ban samu rahoton sace-sace ko kashe mutane ba. Wannan abu yana damu na. Wani lokacin na kan gaza bude wayata saboda na san abin za’a fada min .”

Ya kara da cewa ya dauki akalla jami’an sintiri 1,500 da aka zabo daga kananan hukumomi takwas domin inganta tsaro a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Smolly United za ta yi bikin cika shekaru 9 da kafuwa

Kungiyar kwallon kafa ta Smolly United FC Dambatta za...

Cigaban Kano: Murtala Sule Garo Ya Fadawa Ganduje da Kwankwaso Gaskiya

Tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomin na jihar Kano kuma dan...

Majalisar dokoki ta karbi korafi kan tsawaita wa’adin aiki ga shugaban ma’aikata da wasu da gwamnan Kano ya yi

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi...

Da ɗumi-ɗumi: Ogan Ɓoye ya nada sabbin hadimai 60 a karamar hukumar Nassarawa.

Daga Sidiya Abubakar   Shugaban karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano,...