NAFDAC ta bayyana dalilan da suka sa ake kimatar kayan abincin Najeriya a kasashen waje

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nigeria (NAFDAC) ta gano cewa rashin bin ka’idoji da shawarwarin da hukumar take baiwa masu fitar da kayan abinci zuwa kasashen waje ne yasa ƙasar Ingila take kin amincewa da kayiyakin abinchin da aka kai musu daga Nigeria.

Daga cikin shawarwarin da Nafdac take baiwa masu fitar da kayan abincin har da aka kafa da kuma rashin son masu fitar da tsaftar muhalli da dai sauransu su.

Talla

Kadaura24 ta rawaito Darakta Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Abuja, inda ta bayyana cewa hukumar ta gudanar da wani taro da hukumar kula da ingancin abinci ta kasar Birtaniya, domin dakatar da kin amincewa da kayayyakin abincin Najeriya a kasuwannin duniya.

Hukumar NAFDAC a farkon wannan shekarar ta bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na kayan abinci da ake fitarwa daga Najeriya ana watsi da su a kasashen waje.

Yanzu-Yanzu: Tinubu ya Nada Sabon Shugaban hukumar Aikin Hajji NAHCON

Hukumar ta ce saukaka kasuwancin fitar da kayayyakin da aka kayyade daga Nigeria zuwa kasashen waje ne ya haifar da matsalar da a yanzu ta zama abin damuwa ga Nigeria.

Adeyeye ta ce an gudanar da taron ne a yayin taron karawa juna sani da aka kammala kwanan nan kan hadin gwiwar bunkasa cinikayya da zuba jari tsakanin Najeriya da Birtaniya a birnin Landan, wanda aka shirya karkashin shirin kasuwanci na kasar Birtaniya tare da tawagar Najeriya karkashin jagorancin ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari ta tarayya.

Talla

Adeyeye ta kuma bayyana cewa ta samu wakilcin Darakta mai kula da kula da tashoshin jiragen ruwa da kuma shugaban ofishin kasuwanci da huldar kasa da kasa, Dr Abimbola Adegboye a wajen taron.

 

Domin tinkarar kalubalen, hukumar ta ce zata fara aiwatar da wasu matakai guda shida don magance matsalolin .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin...

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...