Daga Rahama Umar Kwaru
Shugaban kasar Nigeria Bola Tinubu ya amince da nadin Alhaji Jalal Ahmad Arabi a matsayin shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) na tsawon shekaru hudu (4) .
Shugaban ya umarci shugaban hukumar mai barin gado Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya tafi hutun watanni 3 kafin ya yi ritaya kamar yadda dokar ma’aikatan gwamnati (PSR) 120243 ta tanadar daga ranar 18 ga Oktoba, 2023, wanda ya kai ga a ƙarshe ya yi ritaya daga aiki a ranar 17 ga Janairu, 2023.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka aikowe manema labarai.
Bude Boda: Yadda Aka Sami Rashin Jituwa A Majalisar Dattawan Nigeria
Sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Alhaji Jalal Ahmad Arabi, zai fara aiki a ranar 18 ga Oktoba, 2023, kuma zai rike jagorancin hukumar har na tsawon shekaru hudu.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya kuma amince da rusye hukumar zartarwa ta NAHCON.

Shugaban ya yi fatan sabbin shugabannin hukumar ta NAHCON za su yi aiki cikin tsoron Allah tare da kiyaye ka’idojin aiki kamar yadda Alkur’ani mai girma ya fada.