Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar tsaro ta farin kaya wata DSS ta saki Fiddausi ‘yar TikTok
Rundunar tsaro ta DSS a Jihar Kano ta sallami matashiyar jarumar TikTok Fiddausi Ahmad.
Fiddausi dai ita ce wacce ta wallafa faifan bidiyo tana barazanar hallaka alkaliyar da ta jagoranci shari’ar zaben gwamnan Kano da wasu kusoshin gwamnatin Najeriya.

Bayan kamata iyayen ta sun garzaya gidan Radio Freedom don Kai kokensu , sannan suka roki hukumar ta DSS da ta yiwa fiddausin afuwa akan laifin da ta yi.
Yanzu-Yanzu Gwamnan Kano Abba Kabir ya sake sabbin nade-naden mukamai
Rahotanni sun tabbatar da cewa Rundunar ta DSS sai da ta kunnen Fiddausi sannan daga bisani suka sallameta, Inda yanzu haka dai tana gida.