Daga ACP Deniel Itse Amah
Ya Shugabana Kwamishinan yan sanda,
Ina fatan wannan sakon ya same ka cikin koshin lafiya.
Ko da yake an Maida ni jihar Legas babu jimawa ka karbi ragamar hukumar ‘yan sandan jihar Kano , amma na kan bibiyi harkokin tsaron jihar Kano karkashin jagorancin ka ya Shugabana.
Kalubalen da aka fuskanta a jihar, musamman ayyukan “Yan dabba”, abun dubawa ne. Dabarun da ka kirkiro na shirya wasannin kwallon kafa tsakanin jami’an yan sanda da tubabbun ‘yan daba da Kuma gudanar da wasan tsakanin yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki, sun takara rawa sosai wajen kara kyautata alaka tsakanin jami’an yan sanda da al’ummar jihar kano.

Kwarewar da ka nuna wajen dakile tashe-tashen hankula bayan zabukan 2023, musamman idan akai la’akari da zazzafar hamayyar siyasar dake tsakanin manyan jam’iyyun siyasa a kano, ya nuna tsantsar kwarewarka , wanda hakan ya baka damar fita Kunya daga yadda al’ummar jihar kano da na kasa baki daya suka zuba idanu a gare ka don ganin yadda zaka tabbatar da zaman lafiya a wadanca lokuci mai sammatsi .
Yanzu-Yanzu Gwamnan Kano Abba Kabir ya sake sabbin nade-naden mukamai
Jagorancin ka musamman bayan hukuncin kotun, ya nuna kwazon ka, hangen nesa, da jajircewarka ga kokarin tabbatar da zaman lafiya. Hazakarka ta tabbatar da bin doka tasa al’ummar Nigeria da na kasashen duniya suna yaba maka .
Majalisa ta gargaɗi Tinubu kan kashe kudade ba bisa ƙa’ida ba
A matsayina na ƙaramin jami’in dan sanda da har yanzu nake neman kwarewa wannan aiki, na ɗauki kaina mai sa’a da na ɗauke ka a matsayin jagora kuma wanda nake kwaikwayo. Hikima da gogewar da kake kawowa wajen inganta tsaro, tasa ina alfahari da samun ka a matsayin shugaba a wannan aikin. Ina sha’awar ci gaba da da yin amfani da tarin ilimin da kake da shi.
Duk da yake alakar mu ba kamar ta baya ba, amma zan dade ina girmamaka da sha’awar sadaukarwarka da salon jagorancin ka . Na yi alkawarin ci gaba da yin biyayya a gare ka da kuma fatan zamu kasance tare a nan kusa.
Ranka ya dade,. Jama’ar Kano, da ma Nigeria, zasu cigaba da kasancewa cikin alfahari da salon jagorancin ka.
Ranka ya dade, Ina yi maka fatan alkhairi,
ACP Daniel Itse Amah,
Commanding officer,
A’a. 23PM,
FHQ Annex,
Lagos.