Cire tallafin mai: Yadda ta kasance a ganawar gwamnatin tarayya da kungiyar ƙwadago

Date:

 

An tashi ba tare da an cimma wata matsaya ba a ganawar da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, a ranar litinin.

 

Taron wanda ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong ya kira, ya gaza magance ko daya daga cikin batutuwan da kungiyar ta gabatar a matsayin dalilanta na tafiya yajin aiki.

Talla

Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan kammala taron, Lalong ya bayyana fatansa na cewa duk da cewa ba za a iya magance matsalolin da ma’aikatan Najeriya ke bukata ba, amma za a warware mafi yawan damuwarsu kafin wa’adin da suka bayar ya cika.

“Na gamsu kuma na yaba da irin rawar da NLC ke takawa wajen kare hakki da jin dadin ma’aikatanmu.

Yanzu-Yanzu: Kotu ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Zaɓen Gwamnan Kano

“Kwazon ku da bayar da shawarwari ba tare da gajiyawa ba, suna da muhimmanci wajen tsara yanayin aiki na gaskiya da haɗa kai da kuma tabbatar da jin daɗin ma’aikatanmu.

“Babu wani abu da aka yi a kan batun bayar da albashin ma’aikata ko kuma batun ASUU. Duk da haka, mun yi imanin cewa daga yanzu zuwa ‘yan kwanaki masu zuwa, lokacin da wa’adin zai ƙare, wani abu zai faru wanda zai sa a sami daidaito.”

Ya ce bisa la’akari da wa’adin da kungiyar ta bayar, idan har ba a samu ci gaba ba kafin cikar wa’adin, to ku fara yajin aikin sai baba ya ganin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...