Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gudanar da wani sintirin a sassan birnin Kano don nuna ƙarfin da take da shi wajen tunkarar abin da ta kira “kowacce irin barazana”.
An ga kwambar motocin haɗin gwiwar jami’an tsaro da suka haɗar da ‘yan sanda da sojoji da kuma sauran jami’ai masu kayan sarki yayin wannan sintiri da suka zagaya sassan birnin kasuwancin.
![](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2023/09/IMG-20230626-WA0011-232x300.jpg)
Jami’an dai na wannan shiri ne da kuma jan kunne a ranar jajiberen hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano, za ta yanke a ranar Laraba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Hussain Muhammad Gumel ya shaida wa BBC cewa sun yi tsare-tsare don tabbatar da ganin ba a samu asarar rai ko dukiya ko kuma cin zarafin wani mutum ba, bayan sanar da hukuncin kotun.
Tarihin Alƙaliyar Kotun da Zata Yanke Hukuncin Zaben Gwamnan Kano
“Dangane da bayyana wannan hukunci, ko da ta yi daɗi gare shi, ko ba ta yi daɗi gare shi ba”.
Ya ce jami’an tsaro za su tabbatar da samar da ingantaccen tsaro a ciki da wajen harabar kotun da za ta yi wannan hukunci. CP Hussain Gumel ya ce duk mutumin da zai shiga kotun, sai ‘yan sanda sun tantance shi, sannan an caje shi lokacin da ya je domin halartar zaman yanke hukuncin.
Rundunar ta ce tuni ta tura isassun jami’an tsaro da kayan aiki zuwa wuraren da ta shaida a matsayin muhimmai a Kano don tabbatar da tsaron rayuka da na dukiya, a ƙoƙarin wargaza duk wani yunƙuri na kawo hargitsi da karya doka da oda.
‘Yan sandan sun kuma fitar da jerin shawarwari ga mazaunan jihar ciki har da:
– Gujewa taro ko shiga duk wani taron masu haddasa tarzoma ko jerin gwano ko zanga-zanga da murnar da za ta iya haddasa rikici.
Cire tallafin mai: Yadda ta kasance a ganawar gwamnatin tarayya da kungiyar ƙwadago
– Sai mutanen da ke da cikakken katin shaida ne za a bai wa damar shiga harabar kotun sauraron ƙararrakin zaɓen Kano.
– Kyamarori da wayoyi da duk wata na’urar aika bayanai game da hukuncin na iya zama raina kotu, kuma za a hukunta waɗanda suka take wannan umarni, in ji ‘yan sanda
– Furta kalamai ba tare da linzami ba na iya haddasa tunzurin babu gaira babu dalili, ko kuma yin zagon ƙasa ga harkokin tsaro da kuma mutuncin kotu.