Daga Safwan Suraj Iliyas
Kotun sauraron kararrakin zabe ta sanya ranar Laraba 20 ga watan Satumba domin yanke hukuncin Shari’ar kujerar Gwamnan Kano.
Kadaura24 ta rawaito Idan za’a iya tunawa bayan kammala zaɓen gwamnan jihar kano wanda hukumar zabe ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben, hakan tasa jam’iyyar APC ta shigar da Kara gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar domin ƙalubalantar zaben.
A cikin wata sanarwa da ta fito daga Kotu sauraren kararrakin zaben Mai dauke da sa hannun maga takardar kotu , tace za’a gudanar da zaman yanke hukuncin ne a babbar Kotun jihar kano dake Miller Road a Kano.
Da dumi-dumi: Kotu ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Zamfara
Hukuncin kotun dai shi zai tabbatar da halastaccen wanda ya ci zaɓen, duk kuwa da cewa akwai damar daukaka kara ga duk wanda bai aminta da hukuncin kotun sauraren kararrakin Zaben gwamnan ba .
Yanzu haka dai al’ummar jihar Zamfara suna dakon zuwan ranar litinin din domin hukuncin da kotun zata zartar.