Daga Rahama Umar Kwaru
Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta yi Allah wadai da barazanar kisa da kwamishinan kasa da safayo na jihar kano, Adamu Aliyu Kibiya ya yi wa alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano, inda ta bayyana hakan a matsayin cin zarafi ga bangaren shari’a da ba za a yi wasa da shi ba.
A wani bidiyo da jaridar kadaura24 ta gani a shafukan sada zumunta, kwamishinan kasar, Adamu Aliyu Kibiya a ranar Alhamis din da ta gabata a wani taron addu’a na musamman da magoya bayan jam’iyyar NNPP suka gudanar ya zanta da ‘yan jaridu, inda ya yi barazana ga alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da cewa duk wanda a cikin su ya karbi cin hanci to ya zaba ko kudi ko kuma rayuwarsa.
Da yake mayar da martani kan lamarin, shugaban kungiyar lauyoyin reshen Kano, Barr. Suleiman Gezawa ya shaida wa SOLACEBASE a ranar Juma’a cewa ya kamata gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sanyawa kwamishinan takunkumi domin ya nuna cewa maganar ba matsayar gwamnatin jihar ba ce.
‘’ Hankalina kawai ya karkata ga labarin barazanar kisa da wani dan majalisar zartarwa na jihar Kano ya yi wa alkalan kotun sauraron kararrakin zabe da ke cewa idan daya daga cikinsu ya karbi cin hanci to alkali ya shirya zabar kudi ko ransa. , ”In ji Gezawa.
”Wannan ba abin yarda ba ne kuma ba za mu bar shi ya tafi haka ba. Mu a kungiyance muna kira ga gwamna da ya sanya masa takunkumi domin nisanta kansa da gwamnati daga irin wannan furucin.’’
Gezawa ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su binciki wannan barazanar domin akwai barazanar kisa da kwamishinan ya yayi a fili wacce bata dace ba.
Shugaban kungiyar lauyoyin ya kara da cewa wannan shi ne mataki na farko da hukumar ta dauka domin za ta dauki mataki na gaba idan ba a yi komai ba kan lamarin.