Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ke Abuja za ta yanke hukunci kan kararrakin da ke kalubalantar zaben shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba 6 ga watan Satumba kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.

A watan Mayu, SaharaReporters ta ruwaito cewa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta hade kararrakin da jam’iyyun siyasa daban-daban suka shigar gabanta a yayin da take gabatar da rahoton gabanin sauraron karar tare da gabatar da jadawalin shari’ar.
Haka kuma ta tanadi hukunci kan karar da jam’iyyar APM da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP suka shigar domin yanke hukuncin a rana daya da ta Peter Obi na jam’iyyar Labour.

A kwanan baya, ta musanta cewa ta sanya ranar 16 ga watan Satumba domin yanke hukunci.